Za a ci gaba da gasar Turkiya cikin watan Yuni

Turkey League

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Gasar Turkiya tsakanin Galatasay da Besiktas
An wallafa

Hukumar kwallon kafar Turkiya ta ce ta shirya karbar bakuncin wasan karshe a gasar Champions League ta bana, wadda Uefa ta dage a baya saboda bullar cutar korona.

A wata biyu da suka wuce ne hukumar kwallon kafar Turai, Uefa, ta dakatar da wasan karshe na Champions League wanda aka tsara yi a Instanbaul cikin watan Mayu.

Shugaban hukumar kwallon kafar Turkiya, Nihat Ozdemir ya ce sun shirya don ci gaba da gasar Turkiya daga ranar 12 ga watan Yuni da fatan karkare kakar 2019-20 ranar 26 ga watan Yuli.

Za kuma a dunga wasa bakwai a karshen mako da guda daya a cikin makon. kuma kungiyoyi za su buga wasanninsu a filayensu, ya kuma ce babu batun karkare kakar bana a birni daya in ji Ozdemir.

''Muna fatan kammala gasar kwallon Turkiya cikin watan Yuli mu kuma bai wa zakara kofi a cikin fili, sannan mu karbi wasan karshe a gasar Champions League cikin watan Agusta''.