Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Madrid da Barcelona na son Sancho, United ta fi son Grealish
Manchester United ta fi son daukar dan wasan tsakiyar Aston Villa, Jack Grealish mai shekara 24 sama da James Maddison na Leicester City mai shekara 23, a cewar jaridar Manchester Evening News.
Real Madrid da Barcelona sun fara rige-rigen sayen dan wasan gaban Borussia Dortmund, Jadon Sancho. Man United ma ta matsa wurin daukar dan wasan gefen mai shekara 20 dan kasar Ingila. (Bild)
Arsenal na fuskantar matsi daga kungiyar AC Milan wurin daukar dan wasan tsakiyar kasar Faransa da kungiyar Real Betis, Nabil Fekir mai shekara 26. (Marca)
Bayern Munich na da niyyar biyan fan miliyan 60 ne kawai kan Leroy Sane, dan wasan gefen Manchester City da Jamus mai shekara 24. (Sky Sports)
Barcelona ba za ta sayar da Philippe Coutinho ba kan abin da ya gaza yuro miliyan 100. Ana alakanta dan wasan kasar Brazil din mai shekara 27 da kungiyar Chelsea. (Mundo Deportivo)
Inter Milan na son ta sayi dan wasan bayan Chelsea, Victor Moses wanda ke buga mata wasa aro yanzu haka, amma tana so Chelsea ta rage farashin yuro miliyan 12 da ta nema kan dan wasan Najeriya. Calciomercato)
Manchester City ta soma tattaunawa da Barcelona a kan dauko dan wasan Portugal Nelson Semedo, mai shekara 26. Yarjejeniyar za ta kai ga mika wani dan wasan na Portugal Joao Cancelo, mai shekara 25 ga Barca. (Sport)
Dan wasan Brazil Fernandinho, mai shekara 34, yana son sabunta kwangilarsa a Manchester City. (Sky Sports)
Dan wasan Bournemouth da Scotland Ryan Fraser, mai shekara 26, yana son komawa Tottenham idan kwangilarsa ta kare a bazara. (Football Insider)
Shugaban kwallon kafar Arsenal Raul Sanllehi ya shaida wa ma'aikatan kungiyar cewa musayar 'yan kwallo ba ta cikin shirinsa na wannan bazarar. (Standard)