Za a gurfanar da Nasser Al-Khelaifi da Jerome Valcke kan cin hanci

Nasser Al-Khelaifi (right of Jerome Valcke) has been president of PSG since 2011

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Za a gurfanar da shugaban Paris St-Germain, Nasser Al-Khelaifi da tsohon sakatare janar na Fifa, Jerome Valcke a Satumba kan zargin cin hanci.

Ana zargin mutanen biyu da karbar na goro wajen bayar da damar tallata wasannin Fifa a kafar yada labarai.

Akwai wani mutum na uku da ba a sanar da sunansa ba da ake zargi da yin shugabanci ta hanyar da ba ta dace ba da samar da takardu na jabu.

Za a saurari karar a Bellinzona, Switzerland.

Ana zargin Al-Khelaifi wanda ke kuma shugabantar rukunin kafar yada labarai ta BeIN, da laifin bayar da na goro ga Valcke domin a bai wa kamfaninsa damar tallata wasannin Fifa har da Gasar Kofin Duniya.

Sai dai kuma a watan Fabrairu ofishin mai shigar da kara a Switzerland wato atoni janar ya soke zargin da ake yi wa Al-Khelaifi na neman nuna gasar kofin tuniya ta 2026 da ta 2030 a kafar yada labarai, bayan da suka cimma yarjejeniya.

Ana zargin Valcke da amfani da matsayinsa a hukumar kwallon kafa ta duniya tsakanin 2013 da 2015 da tursasawa a bai wa Italiya da Girka damar nuna wasu Gasar Kofin Duniya a talabijin a wasannin 2018 da na 2030, shi kuma ya amince da karbar na goro ta hannun wani attajiri.

Dukkan mutanen sun musanta zargin da ake yi musu.