Rooney ya ce shi ba kwararren mai cin kwallaye ba ne

Asalin hoton, Getty Images
Dan wasan Ingila da Manchester United, Wayne Rooney ya ce ya kamata ya ci kwallaye fiye da wadanda ya zura a raga duk da shi ba kwararre ba ne a fannin.
Rooney ya ci kwallo 253, hakan ya sa ya doke tarihin da Sir Bobby Charlton ya kafa na cin kwallaye da yawa a United, ya kuma haura shi a ci wa tawagar Ingila kwallaye, bayan da ya zura 53 a raga.
"Ni ban kai kwarewar Gary Lineker ko kuma Ruud van Nistelrooy wajen iya cin kwallaye ba."
Bayan da ya Rooney ya taka rawar gani a Everton ne ya koma Manchester United da taka leda yana mai shekara 16 a 2004, daga nan ya yi wasa 559 a kungiyar.
Haka kuma dan kwallon ya buga wa tawagar Ingila wasa 120.
"Na kafa tarihin yawan ci wa Manchester United da tawagar Ingila kwallaye ina mai alfahari da hakan duk da cewar akwai wadanda suka fi ne kwarewa."
"Na yi shekara 13 a United na buga wa tawagar Ingila wasa shekara 15. Na kuma samu lokacin da na kafa tarihin cin kwallaye - idan na tuna baya sai naga ya kamata na zura fiye da wadanda na ci a yanzu."
Rooney wanda yanzu yake matakin koci kuma dan wasa a Derby County ya ce Harry Kane zai yi bajintar da za a dunga tunawa da shi a tawagar kwallon kafa ta Ingila.
Ya kuma kara da cewar tarihin da ya kafa a United zai dade ba a samu mai karya shi ba, ganin 'yan kwallon yanzu ba sa dade wa a kungiya daya, sai dai ya ce da Lionel Messi ko kuma Cristiano Ronaldo za su dawo Old Trafford to da cikin shekara uku za su shafe tarihin da ya yi.












