Watfod ta hana Liverpool cin wasan Premier na 19 a jere

An wallafa

Fatan da Liverpool ke yi na buga wasannin Premier bana ba tare da an doke ta ba ya zo karshe, bayan da Watford ta yi nasara a kanta a Vicarage Road.

Kungiyar da Jurgen Klopp ke jan ragama ta so kafa tarihin cin wasan Premier 19 a jere, amma sai ta kasa tabuka wa a gidan Watford.

Watford ta yi nasarar doke Liverpool da ci 3-0 a wasan mako na 28 da suka fafata ranar Asabar.

Isma'ila Sarr ne ya ci biyu a karawar, sannan ya bai wa kyaftin Troy Deeney kwallon da ya ci na uku, bayan da suka yi minti 45 babu wadda ta sa kwallo a raga.

Kuma karon farko da dan wasa ya ci biyu ya yi sanadin ta uku a wasa daya a manyan gasar Turai biyar a fafatawa 108 da aka yi.

Kuma dan kwallo na farko da ya yi sanadin cin uku a raga ko fiye da haka a fafatawa da Liverpool a gasar Premier tun bayan bajintar da Harry Kane ya yi a Oktoban 2017.

Karon farko da aka ci Liverpool a gasar Premier, bayan da ta yi kwana 422 da wasa 44 ba a doke ta ba.

Kungiya ta biyu a tarihi da ta yi wannan bajintar, wadda rabon da a doke ta tun ciikin watan Janairun 2019.

Haka kuma tun 1-1 da ta buga da Manchester United a Old Trafford ranar 20 ga watan Oktoba 2019, Liverpool ta ci wasa 18 a Premier a jere.

Haka kuma kocin Watford, Nigel Pearson shi ne mai horas wa dan Ingila da ya doke Liverpool a gasar Premier, tun bayan Sam Allardyce da ya yi a kungiyar Crystal Palace a Afirilun 2017.

Da wannan sakamakon Liverpool tana nan a matakinta na daya da maki 79, sai Manchester City ta biyu da maki 57,sannan Leicester City ta uku da maki 50.

Ita kuwa Leicester City wadda take cikin 'yan kasann teburin kan ta kara da Liverpool, yanzu ta koma ta 17 da maki 27.

Wasanni shida da ke gaban Liverpool

FA CUP3 ga watan Maris

  • Chelsea da Liverpool

Premier League 7 ga watan Maris

  • Liverpool da Bournemouth

Champions League 10 ga watan Maris

  • Liverpool da Atletico Madrid

Premier League 16 ga watan Maris

  • Everton da Liverpool

Premier League 21 ga watan Maris

  • Liverpool da Crystal Palace

Premier League 5 ga watan Afirilu

  • Man City da Liverpool