Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Liverpool ta bai wa City tazarar maki 19 a Premier
Liverpool ta yi nasarar doke West Ham United da ci 2-0 a kwantan wasan gasar Premier da suka fafata ranar Laraba.
Liverpool ta fara cin kwallo ne a bugun fenariti ta hannun Mohamed Salah saura minti 10 a je hutu.
Bayan da 'yan wasa suka sha ruwa ne aka koma zagaye na biyu Liverpool ta kara na biyu ta hannun Oxlade-Chamberlain.
Da wannan sakamakon Liverpool mai maki 70 ta daya a teburin Premier ta bai wa Manchester City ta biyu tazarar maki 19.
Kungiyar ta Anfield ta ci wasa 23 kenan da canjaras daya, har yanzu ba a doke ta ba.
West Ham kuwa tana ta 17 da makinta 23, bayan buga wasa 24.
Haka kuma Liverpool ta zura kwallo 56 a raga, ita kuma guda 15 suka shiga ragarta.
A ranar Asabar 1 ga watan Fabrairu, Liverpool za ta karbi bakuncin Southampton a wasan mako na 25 a gasar ta Premier.
Haka kuma matasan Liverpool za su karbi bakuncin Shrewsbury Town a wasa na biyu kuma a zagaye na hudu a FA Cup.
Karawar farko da Liverppol ta ziyarci Shrewsbury 2-2 suka yi, dadlin da ya sa za su sake karawa ranar 4 ga watan Fabrairu.