Premier League: Liverpool ta doke Tottenham har gida

An wallafa

Liverpool ta zama kungiya ta farko da ta ci wasan lig 20 cikin 21 na farko a gasar lig ta manyan kasashen Turai guda biyar (Ingila, Sifaniya, Jamus, Italiya, Faransa), bayan ta doke Tottenham har gida.

Yanzu haka ta bayar da tazarar maki 16 a saman teburi tare da kwantan wasa guda daya, Roberto Firmino ne ya tabbatar da hakan da kwallon da ya ci guda daya tilo a filin wasa na Tottenham Hotspur.

Sai dai tawagar Joise Mourinho ta yunkura amma hakanta bai cimma ruwa ba, wadda ta yi wasa babu tauraron dan wasanta Harry Kane.

Da alama jiran shekara 30 da Liverpool ta yi ba tare da lashe kofin Premier ba ya zo karshe, ganin yadda take ci gaba da kafa tarihi - ta ci kwallo a dukkanin wasa 21 da ta buga na kakar bana.

Karawa tsakanin kungiyoyin

  • Babbar nasarar da Tottenham ta taba samu a kan Liverpool a wasa 14 na baya-bayan nan ita ce 4-1 a filin wasa na Wembley a watan Oktoban 2017 - canjaras 4, rashin nasara 9.
  • Wasa daya kacal Liverpool ta gaza ci cikin bakwai a gidan Tottenham (canjaras 2, nasara 4) bayan ta doke ta sau biyar a jere a Anfield.

Tottenham

  • Wasan Premier daya kacal Tottenham ta ci cikin hudu (canjaras 1, rashin nasara 2)
  • Ba ta ci wasa ko daya ba a cikin 11 tsakaninta da manyan kungiyoyi shida (canjaras 3, rashin nasara 8)

Liverpool

  • Liverpool ta ci wasa 12 a jere na Premier a baya-bayan nan, inda ta ci kwallo 29
  • Wasa 20 da kuma canjaras daya da ta yi a wannan kakar cikin wasa 20 ya zama na biyu a tarihi tun bayan wanda Man City ta kafa a kakar 2017-2018.
  • Liverpool ta zama kungiya ta farko da ta cinye wasanta 20 na farko cikin 21 a manyan gasar lig biyar ta kasashen Turai