La Liga: Real Madrid ta casa Getafe har gida

Asalin hoton, Getty Images
Real Madrid ta casa Getafe har gida da ci 0-3 a wasan La Liga mako na 19, inda kuma ta dare saman teburin gasar kafin Barcelona ta buga wasan hamayya da Espanyol a yau Asabar.
Kuskuren da mai tsaron ragar Getafe Soria ya yi ne, bayan ya ji matsi daga Raphael Varane, ya bai wa Madrid kwallonta ta farko a minti na 34.
Varane ya dauki ragamar bayan Madrid ne sakamakon rashin kyaftin Sagio Ramos sannan kuma da shi aka rika kai hari.
Shi ne dai ya kara ta biyu bayan ya saka wa kwallo kai daga wani bugun tazara da Tony Kroos ya bugo a minti na 53.
Ya kamata Gareth Bale da Vinicius Junior su ci kwallo bayan kowannensu ya samu dama daga shi sai gola - Vinicius ya buga ta waje, Soria kuma ya bige ta Bale zuwa waje, bayan ya yi yunkurin yanke golan.
A minti shida na karshe da aka kara ne kuma Madrid suka zari kwallo tun daga gidansu, inda Federico Valverde bai so kansa ba, ya bai wa Modric shi kuma ya saka ta uku.
Wannan sakamakon ya sa Getafe ta koma matsayi na bakwai a teburin La Liga.
Madrid kuwa ta dare saman teburin ne kafin sakamakon da Barca za ta samu a wasan hamayyar Kataloniya tsakaninta da Espanyol da karfe 9:00 agogon Najeriya.









