Matsalar tsaro: Mali ta fara taron neman mafita.

Asalin hoton, AFP
Shugaban Mali Ibrahim Boubacar Keita ya bude wani taron kasa a babban birnin Bamako, domin samo mafitar siyasa da kuma ta soji kan matsalar tsaro daga masu ikirarin jihadi a kasar.
Shugaba Keita ya shaida wa dubunnan masu halartar taron cewa lokaci ya yi da za a hada kai domin kawo karshen rashin zaman lafiyar daga masu ikirarin jihadi.
Wasu daga cikin kungiyoyin 'yan bindiga daga arewacin kasar da suka hada da mayakan Tuareg, wadanda suka sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya ta shekarar 2015 a kasar, sun samu damar halartar taron.
Masu ikirarin jihadi da ke da nasaba da kungiyar Alka'ida da kuma IS dai sun kai hare-hare a yankin Sahel na yammacin Afirika, tare da kashe akalla sojoji 230 cikin watanni 4 da suka gabata.
Ko a ranar talatar da ta gabata ma, an kashe sojojin kasar Nijar sama da 70.








