FIFA: Najeriya ta matsa gaba a duniya

Tawagar Super Eagles

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Tawagar Super Eagles
An wallafa

Super Eagles ta Najeriya ta tsallaka matsayi na 31 cikin jerin kasashen da suke gaba-gaba a duniya a harkar tamaula.

A baya dai kungiyar na a mataki na 35 a rahoton da hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta saba fitarwa a kowanne wata.

Rahoton hukumar FIFA dai ya nuna cewa kungiyar ta Super Eagles na a mataki na uku a nahiyar Afirka bayan da ta bi bayan kasashen Senegal wadda take a matsayi na farko da kuma Tunisia da ke bi mata.

Algeria na bayan Najeriya yayinda ta fada matsayi na hudu a Afirka.

Sai dai Indomitable Lions ta kasar Kamaru ta fuskanci koma baya bayan da ta koma mataki na 53 yayin da take 52 a duniya.

Kamaru ta kasance a mataki na 8 a Afirka, wato dai tana bayan Masar wadda take a matsayi na bakwai, inda kasar Marocco ke na biyar .

Kasar Belgium ce ta daya a duniya, inda Faransa ke bi mata a mataki na biyu, Ingila na bayan Brazil a mataki na hudu.