Champions League: Kungiyoyi uku ne suka san makomarsu a zagaye na 16

Kwallon Aaron Ramsey ta taimaka wa Juventus sanin matsayarta

Asalin hoton, BBC Sport

Bayanan hoto, Kwallon Aaron Ramsey ta taimaka wa Juventus sanin matsayarta
An wallafa

Yayin da kungiyoyi uku suka sami tikitin zagaye na 16 a Gasar Zakarun Turai, yanzu haka akwai gurbin kungiyoyi 13 da ke ajiye.

Bayern Munich da Juventus da kuma Paris St-Germain ne kungiyoyi na farko da suka fara fitowa zagaye na 16 a gasar bana bayan da suka nuna bajinta a wasanninsu.

Yayin da zagaye biyu ya rage a kammala wasan rukuni, ko wacce kungiya ce za a yi waje da ita?

Kulob-kulob din Premier hudu na iya samun gurbi a zagaye na 16 a Gasar Zakarun Turai da za a yi cikin makon nan.

Wasanni biyu ne suka rage kungiyoyin da suka cancanta su fito daga gurbi.

Abin da kungiyoyin Premier ke nema a wannan makon:

  • Tottenham: Za ta iya fitowa daga rukuni idan har ta samu galaba a kan Olympiakos ranar Talata, ko kuma idan suka yi canjaras matsawar Red Star Belgrade ta gaza samun nasara a kan Bayern Munich.
  • Manchester City: Nasara take nema a kan Shakhtar Donetsk kuma hakan zai sanya ta kasance jagaba a rukuni na uku. Canjaras ma dai zai ba ta damar fitowa.
  • Liverpool: Nasara take nema a kan Napoli ranar Laraba domin kasancewa zakara a rukuni na biyar. Idan Salzburg ta gaza samun nasara a kan Genk, Liverpool za ta fito daga rukuni kodayake ya danganta da makin da ta samu a kan Napoli.
  • Chelsea: Za ta iya kai wa zagaye na 16 idan ta samu nasara a kan Valencia yayin da take neman nasara a wasanninta biyu da suka rage, amma ya danganta da irin makin da kungiyoyin da ke kasanta suka samu.
Rukunin farko

Asalin hoton, BBC Sport

Bayanan hoto, Rukunin farko

Mai rike da kambun kofin Ligue 1 a kasar Faransa PSG ce kan gaba a saman teburi a rukuni na daya, bayan da ta ci wasanni hudu, inda ta zura kwallo 10 a raga, kuma har yanzu ba a zura mata ko da kwallo daya ba.

Real Madrid wadda ta taba lashe gasar sau 13 a baya, ita ke na biyu a saman teburi a rukunin wato maki biyar kenan tazara tsakaninta da Club Bruges inda kungiyar Galatasaray ta kasar Turkiyya take matakin karshe da maki daya tilo.

Sauran wasannin da suka rage:

Talata, 26 ga Nuwamba - Galatasaray da Bruges, sai Real Madrid da PSG

Laraba, 11 ga Disamba - PSG da Galatasaray, Bruges da Real Madrid

Rukunin na biyu

Asalin hoton, BBC Sport

Bayanan hoto, Rukunin na biyu

RUKUNIN (B)

Zakarar Bundesliga Bayern Munich ita ce ta daya a saman teburi da maki 12, inda ta samu nasara a wasanni hudun da ta buga.

Ita kuwa kungiya ta biyu a bara, Tottenham ita ce ta biyu a saman teburi da maki bakwai, maki hudu kenan tsakaninta da Red Star, sai Olympiakos ta karshe da maki daya a saman teburi.

Sauran wasannin da suka rage:

Talata, 26 ga Nuwamba - Tottenham da Olympiakos, Red Star Belgrade da Bayern Munich

Laraba, 11 ga Disambar - Bayern Munich da Tottenham, Olympiakos da Red Star Belgrade

Rukuni na uku

Rukuni na uku

Asalin hoton, BBC Sport

Bayanan hoto, Rukuni na uku

RUKUNIN (C)

Mai rike da kambun kofin Premier Manchester City ta rasa damar maki dayan da take nema duk da cewa yanzu haka itace ta daya a saman teburi da maki 10, sai dai canjaras din da ta yi da Atalanta da 1-1 ya kawo mata cikas, kuma maki biyar ne tsakaninta da kungiyar.

Kulob din Pep Guardiola dai maki daya tilo yake nema domin rike tikitin zagaye na 16.

Shakhtar Donetsk wacce ke matsayi na biyu da Dinamo Zagreb a mataki na uku dukkansu na da maki biyar-biyar, sai Atalanta da ke karshe da maki daya tilo.

Sauran wasannin da suka rage:

Talata, 26 ga Nuwamba - Manchester City da Shakhtar Donetsk, Atalanta da Dinamo Zagreb

Laraba, 11 ga Disambar - Shakhtar Donetsk da Atalanta, Dinamo Zagreb da Manchester City

Rukuni na hudu

Asalin hoton, BBC Sport

Bayanan hoto, Rukuni na hudu

RUKUNIN (D)

Zakarar Serie A Juventus doke Lokomotiv Moscow da tayi da ci 2-1 a rukuni na hudu ya ba ta damar darewa kan teburi da maki 10 a cikin wasanni hudu.

Atlético Madrid ce ta biyu inda ta sha gaban Lokomotiv da Bayer Leverkusen wadanda ke da maki uku-uku.

Kodayake Atletico Madrid na a matsayi mai karfin da zai ba ta damar tsallakawa zagaye na gaba, idan aka kwatanta makinta da sauran kungiyoyin.

Sauran wasannin da suka rage:

Talata, 26 ga Nuwamba - Lokomotiv Moscow da Bayer Leverkusen, Juventus da Atlético Madrid

Laraba, 11 ga Disambar - Atlético Madrid da Lokomotiv Moscow, Bayer Leverkusen da Juventus

Rukuni na biyar

Asalin hoton, BBC Sport

Bayanan hoto, Rukuni na biyar

RUKUNIN (E)

Ita ma dai mai rike da kambun gasar, Liverpool ita ce kan gaba a rukuni na hudu da maki tara a saman teburi, kuma nasara daya take nema da zai ba ta damar tsallakawa zagaye na 16 a gasar.

Napoli wadda ta kasance ta biyu da maki takwas, maki hudu ne tazara tsakaninta da Red Bull Salzburg, inda Genk ke a mataki na karshe da maki daya nasara take nema a wasanninta biyu.

Sauran wasannin da suka rage:

Talata, 26 ga Nuwamba - Liverpool da Napoli, Genk da Red Bull Salzburg

Laraba, 11 ga Disambar - Napoli da Genk, Red Bull Salzburg da Liverpool

Rukuni na shida

Asalin hoton, BBC Sport

Bayanan hoto, Rukuni na shida

RUKUNIN (F)

Zakarar La Liga Barcelona za ta iya kai bantenta a rukuni na shida idan har ta doke Borussia Dortmund a karawar da zasuyi a Camp Nou.

Kodayake kungiyar Dortmund ta kasar Jamus ta samu nasarar doke Inter Milan da ci 2-0 a wasansu na baya, wanda hakan ya ba ta damar samun maki uku, sai dai Slavia Prague ce ta karshe a teburi da maki biyu.

Sauran wasannin da suka rage:

Talata, 26 ga Nuwamba- Barcelona da Borussia Dortmund, Slavia Prague da Inter Milan

Laraba, 11 ga Disambar - Borussia Dortmund da Slavia Prague, Inter Milan da Barcelona

Rukuni na bakwai

Asalin hoton, BBC Sport

Bayanan hoto, Rukuni na bakwai

RUKUNIN (G)

RB Leipzig ita ke jan ragamar rukuni na bakwai, kuma nasara daya take nema a wasannin ta biyu da za ta yi domin samun damar tsallakawa zagaye na 16, Lyon ke bi mata da maki bakwai a teburi inda take neman nasara a kan Zenit St Petersburg a wasan su na gaba.

Sauran wasannin da suka rage:

Talata, 26 ga Nuwamba - Zenit St Petersburg da Lyon, RB Leipzig da Benfica

Laraba, 11 ga Disambar - Benfica da Zenit St Petersburg, Lyon da RB Leipzig

Rukuni na takwas

Asalin hoton, BBC Sport

Bayanan hoto, Rukuni na takwas

GROUP (H)

Rukunin karshe na takwas shi ne ake ganin akwai sarkakiyar kece raini sosai, kodayake Ajax dai ta samarwa kanta mafita, domin ba ya ga maki bakwai da take da shi, akwai bambancin kwallo da ta samu maki biyar a kai sabanin Chelsea da Valencia da ke da maki daya.

Duk da cewa suna da maki bakwai a saman teburi, dama dai kungiyar Lille tuni ta san makomarta da maki daya tilo.

Sauran wasannin da suka rage:

Talata, 26 ga Nuwamba - Valencia da Chelsea, Lille da Ajax

Laraba, 11 ga Disambar - Chelsea da Lille, Ajax da Valencia