Dijon 2-1 Paris Saint Germain: dokewar da ta karshe ta yiwa PSG ta girgiza ta.

An wallafa

Paris St-Germain ta sha kashi karo na uku a gasar Lig 1 a kakar bana, yayin da ta karshe Dijon suka cinye zakarun gasar Faransa.

Dan wasa Kylian Mbappe ne ya fara jefa kwallo ta daya a minti 19 da fara wasan, kuma ita ce kwallo ta bakwai a kakar wasannin ta bana.

Mounir Chouiar ya samu damar dai-daita wasan bayan zare kwallon da ya yi a mintunan karshe kan hutun rabin lokaci.

Daga baya cikin minti na 58 Jhonder Cadiz ya kara jefa kwallo ta biyu wadda ta bawa Dijon nasara a karshen wasan.

Mauro Icardi a kusan mintunan karshe ya buga wata kwallo daga nesa wadda ta kusa shiga sannan Edinson Cavani ya kara buga wa, hakan ya kusa sa su farke kwallonsu.

Wannan nasara da Dijon ta samu, ya sa ta tsallako wuri biyu inda ta dawo ta 18.

PSG, wadda ta lashe Lig 1 sau shida a jere kuma ta jefa kwallaye 17 a wasa hudun karshe da ta buga, ta yi rashin nasara ne kawai sau 5 a kakar 2018-2019, amma a wannan karon har ta yi rashin nasara 3 cikin wasa 12 da aka buga a wannan kakar.

Gaza hada maki 11 da PSG ta yi a ranar Juma'a, zai sa Nantes dake bin ta a baya ta kara rage makin da ke tsakanin su zuwa maki 5 in har ta samu nasara kan Bordeaux a ranar Lahadi.