Watakila Neymar ba zai buga Champions League ba

Asalin hoton, AFP
Dan wasan Paris St Germain, Neymar ya yi rauni a wasan sada zumunta da tawagar Brazil ta tashi 1-1 da ta Najeria a Singapore ranar Lahadi.
Cikin minti 12 da fara tamaula ne Neymar ya fara dingishi, hakan ne ya sa Brazil ta cire shi a wasan ta saka Coutinho wanda ya maye gurbinsa.
Watakila raunin ya hana shi buga wasan Champions League da PSG za ta buga da Club Bruges ranar 22 ga watan Oktoba.
Haka kuma da kyar ne idan Neymar zai yi wa Paris St Germain wasan mako na 10 a gasar Faransa ta League 1 da za ta ziyarci Nice ranar Juma'a.
Neymar ya buga wa Brazil wasa na 101 a fafatawa da Super Eagles, bayan da ya yi na 100 a karawar da suka tashi da Senegal 1-1 ranar Alhamis.
Najeriya ce ta fara cin Brazil ta hannun Joe Aribo mai taka leda a Rangers tun kafin hutu a ranar ta Lahadi.
Bayan da aka koma zagaye na biyu ne Brazil ta farke ta hannun Casemiro mai taka leda a Real Madrid.
Har yanzu Neymar bai buga wasan Zakarun Turai ba a bana, sakamakon hukunta shi da aka yi a fafatawar da Manchester United da fitar da PSG a bara.
An kuma rage hukuncin da aka yanke masa a baya, inda aka ce ba zai yi wasa biyu a bana, kuma bai buga wanda Madrid ta sha kashi a Faransa ba.
Haka kuma Neymar bai buga wasan Zakarun Turai da PSG ta je ta doke Galatasaray ba a cikin watan Oktoba.











