Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Alan Shearer ya ce Manchester United ta tabarbare
Mai fashin baki kan wasan kwallon kafa, Alan Shearer ya ce bai taba ganin lalatacciyar tawagar kulob din Manchester United irin ta yanzu ba bisa la'akari da yadda kulob din Newcastle ya ci Man U daya mai ban haushi, ranar Lahadi.
Tsohon dan wasan Ingilar ya bayyana hakan ne lokacin wani sharhin bayan wasanni da aka saba yi bayan wasan.
Shearer ya ce ta tabbata Manchester United ta samu baraka a bayanta da tsakiyar har ma da gaban nata.
Manchester United dai ta kara cin karo da koma baya a wasannin Premier bana, bayan rashin nasarar da ta yi a hannun Newcastle United.
Shi da kansa kocin Manchester United din, Ole Gunnar Solskjaer ya ce tabbas kulob din nasa ya shiga cikin wani hali na ni-'yasu sakamaon cin rainin da Newcastle United ta yi musu.
To sai dai Solskjaer na da karfin gwiwar cewa a wasan kungiyar na gaba da za ta kara da Liverpool, za su bai wa maras da kunya.
Yanzu dai Manchester United ce ta 12 a kasan teburin Premier da maki tara bayan wasa takwas da ta yi.
Ita kuwa Newcastle United ita ce ta 15 da maki takwas da tazarar maki daya tsakaninta da 'yan ukun karshe a teburin Premier.
Wannan ce kaka mafi muni da Manchester United ta hada maki tara a karawa takwas a gasar Premier tun bayan 1989/90.