Inter Milan ta nada Antonio Conte koci

An wallafa

Inter Milan ta dauki Antonio Conte a matsayin koci bayan ta kori Luciano Spalletti.

Conte mai shekara 49 ya Italiya ne bayan Chelsea ta kori shi a bara.

Ya shafe shekaru biyu a Stamford Bridge, inda ya lashe kofin Premier da FA, bayan kuma ta dauki kofin Seria A sau uku a jere a Juventus.

Karkashin Spalletti, Inter ta kasance ta hudu a tebur, wanda ya ba ta damar tsallakewa zuwa zakarun Turai.

"Zan fara wani babin sabuwar rayuwa," a cewar Conte wanda tsohon dan wasan Italiya ne da Juventus.

Kocin ya yi alkawalin dawo da martabar Inter a Seria A.

Shugaban Inter Milan Steven Zhang ya ce Conte yana cikin fitattun masu horar da 'yan wasa, kuma ya yi imanin zai jagoranci Inter ga nasarori.