'Shekarun daukewar hailar mace ba maita ko surkulle ba ne'
Latsa alamar lasifikar da ke sama don sauraron shirin:
Daukewar jinin haila na cikin abubuwan da mata masu shekarun da suka haura hamsin suke fuskanta.
Wannan ci gaban shirin da muka fara a makon jiya ne.
Wannan al'amari dai ba maita ba ce ko surkule kamar yadda wasu mutane suke tunani a cikin al'umma.
Abu ne da ke faruwa a rayuwar mata masu manyan shekaru.
Alamomin daukewar jinin sun hada da rashin ganin jinin al’ada a kan lokaci da yawan fushi da bushewar fata da rashin barci da kuma rashin son cin abinci.
A wannan makon za mu cigaba da tattauna ne a kan daukewar jinin ga mata masu manyan shekaru.
Za mu duba matakan da mata ya kamata su dauka idan wadannan alamomi sun fara bayanna a tare da su.
Wannan cigaban shirin da muka fara a makon jiya ne.