Kotu ta ba Messi izinin yin kasuwanci da sunansa

An wallafa

Kotun Turai ta ba Lionel Messi, dan kwallon da ya fi samun kudi a duniya, izinin bude kamfani da sunansa domin kasuwancin kayayyakin wasanni.

An shafe shekara bakwai dan wasan na Barcelona da Argentina yana gwagwarmaya a kotu domin samun damar yin amfani da sunansa a kayayyakin wasanni, da suka kunshi tufafi da sauransu.

Messi na son ya fara kasuwanci ne da sunan Massi a matsayin sunan kamfaninsa.

Tun da farko kotun Spain ce ta fara kalubalantar matakin, saboda sunan Massi ya yi daidai da sunan wani kamfani da ke daukar nauyin tseren keke a kasar.

Kotun Spain na ganin babu bambanci a sunayen kuma hakan zai kawo rudani.

Amma a yanzu Messi ya yi nasara a kotun Turai, kuma hukuncin kotun na nufin zai fara amfani da sunansa a kayayyakin wasannin da zai fara kasuwancinsu.

Kotun Turai na ganin kasancewar dan wasan sananne a duniya ba zai kai har a samu rudani ba.

Hukuncin kotun na zuwa a yayin da mujallar kwallon kafa ta Faransa ta fitar da rahoton jerin 'yan wasan kwallon kafa da suka fi kudi a duniya.

Mujallar ta ce Messi ya wuce Ronaldo a matsayin dan wasan da ya fi samun kudi, inda Messi ya samu Yuro miliyan 126 a shekara.

Ronaldo kuma ya samu miliyan 94, a cewar mujallar.

Messi mai shekaru 30, a watan da ya gabata ne ya ci kwallo ta 600 a raga a rayuwarsa wanda kuma ya kasance dan wasan da ya fi cin kwallo a kulub din Barcelona da kasarsa ta Argentina.