Plateau ta fara Firimiya da kafar dama

An wallafa

Mai rike da kofin gasar kwallon kafar Firimiyar Nigeria, Plateau United ta fara wasannin bana da kafar dama.A wasannin makon farko da aka yi a karshen mako ne Plateau United ta je gidan Nasarawa United ta ci ta daya mai ban haushi a ranar Lahadi.Raphael Ayagu ne ya ci wa Plateau United kwallon saura minti uku a tashi daga karawar.Tun a ranar Asabar aka fara gasar Firimiyar Nigeria ta bana inda Katsina United da Kano Pillars suka tashi 2-2.Cikin wasa 10 da aka yi kungiyoyi biyu ne suka ci wasa a waje, haka kuma wadanda suka buga wasan su a waje sun ci kwallo bakwai a raga.Wannan sakamakon daidai yake da wasan farko a gasar bara.Ga sakamakon wasannin makon farko:Kwara 0-2 TornadoesFCIU 2-1 Yobe StarsWikki 1-0 Go RoundAkwa 2-0 RangersLobi 1-1 EnyimbaHeartland 0-0 SunshineNasarawa 0-1 PlateauRivers 1-0 El-KanemiAbia Warriors 2-0 MFMKatsina 2-2 Pillars