Gane Mini Hanya: Yadda aka yi Atiku ya zama ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP
An wallafa
Danna hoton sama ku saurari shirin:
A Najeriya, hankali ya koma kan jam`iyyar APC mai mulki don ganin yada zaben fitar da gwani na masu neman takarar shugaban kasa zai kaya.
A ranar Litinin mai zuwa ne ake sa ran gudanar da zaben fitar da gwanin.
Tuni babbar jam`iyyar hamayya a kasar, PDP ta yi nata zaben, inda tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar ya yi nasara.
Wannan nasara da ya samu, kamar yadda masana siyasa ke cewa, ka iya wargaza lissafin jam`iyyar APC.
Alhaji Adamu Maina Waziri na cikin jiga-jigan PDP, kuma a filinmu na Gane Mini Hanya na wannan makon, Ibrahim Isa ya tattauna da shi a kan yadda zaben fid da gwanin da jam`iyyar tasu ta yi ya kasance da kuma shirin da suke yi na tunkarar APC a babban zaben 2023.