Ra'ayi Riga: Girman matsalar sha da fataucin miyagun kwayoyi a Najeriya

Bayanan sautiRa'ayi Riga: Girman matsalar sha da fataucin miyagun kwayoyi a Najeriya
An wallafa

Danna hoton sama domin kallon bidiyon

A madadin Ra'ayi Riga, Filin A Fada A Cika ya mayar da hankali ne kan girman sha da fataucin miyagun ƙwayoyi a Najeriya.

Najeriya na daya daga cikin kasashen da suka fi ƙaurin suna wajen tuma’alli da miyagun kwayoyi.

Alkalumman Majalisar Ɗinkin Duniya sun nuna cewa Najeriya ta zama tamkar wata tasha da ake safarar miyagun kwayoyi daga yankin Latin Amuruka zuwa Nahiyar Turai da Gabashin Asia da Arewacin Amurka.

Filin ya tattauna da Janar Muhammad Buba Marwa mai ritaya, shugaban hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Najeriya NDLEA.