Lafiya Zinariya: Hatsarin da ke tattare da zubar jini ga mai ciki
An wallafa
Danna hoton da ke sama domin sauraren shirin:
Mata masu juna biyu na samun zubar jini idan mabiyiya ta kasance a kasan mahaifa.
Uwa da jariri kan rasa rayukansu idan ba a dauku matakan da suka dace a kan lokaci ba.
Irin wannan zubar jini kuma na iya sanya mai ciki ta suma.
Sannan idan mabiyiya ta rabu da jikin mahaifa, hakan na iya kai wa ga ciwon koda.
Haka kuma jini na iya zuba ta ko’ina a jikin mai juna biyu ko da kuwa girman hujin bai wuce hudar allura ba.