Gane Mini Hanya: Cikar Mohamed Bazoum shekara guda kan mulki

Bayanan sautiGane Mini Hanya: Cikar Mohamed Bazoum shekara guda kan mulki
An wallafa

Latsa hoton sama domin sauraren hirar

Shugaban Nijar Mohamed Bazoum ya cika shekara ɗaya da zama shugaban Nijar bayan rantsar da shi watan Afrilun 2021.

Yayin wata ganawa da 'yan jaridu, Shugaba Mohamed Bazoum ya bayyana nasarorin da ya ce ya samu a wasu fannoni da suka hada da tsaro da yaki da cin hanci da rashawa a tsawon shekara guda da ya yi yana jan ragamar milkin kasar.

Bazoum ya kuma koka dangane da yadda ake samun yawan hayayyafa ba tare da samar da makoma ga yaran da ake haihuwa barkatai ba.

Sai dai shugaban ya fara da bayani kan halin da ake ciki dangane da matsalar tsaro da batun 'yan gudun hijra, a tattaunawarsa wakiliyar BBC Hausa, Thcima Illa Issoufou a Yamai.