Ra’ayi Riga: Yadda aka koma sauraren wa’azi a kafofin sada zumunta na intanet
An wallafa
Latsa hoton sama domin sauraren shirin
A shekarun baya galibin al'umma kan amfana da falalolin watan Ramadan ta hanyar sauraran rediyo da zuwa wuraren wa'azi ko kuma kunna kaset na radio da malaman da suka kwanta musu a rai suka nada.
Amma cikin ‘yan shekarun nan, zamani ya zo da sabon salo na amfana daga wajen Malamai ta hanyar bibiyarsu a kafofin sada zumunta na intanet kamar su Facebook da Twitter da Instagram da kuma Tiktok.
Filin Ra'ayi Riga na wannan mako ya yi tattaunawa ta musamman kan wannan batu.
Kuna iya aiko mana da takaitattun ra'ayoyinku game da yadda kuke sauraron wa'azi a wannan lokaci.