Lafiya Zinariya: Ko kin san hantara na hana yara tsawo?

Bayanan sautiKo kin san hantara na hana yara tsawo?
An wallafa

Ku latsa lasifikar don sauraron shirin:

Hantara da ke kai wa ga yawan damuwa a rayuwar yaro karami na hana shi ya yi tsawo kamar sauran sa'anninsa. In ji Likitoci

A kimiyance karancin abincin mai gina jiki a jikin yara, musamman 'yan kasa da shekara uku shi ne babban makasudin da ke janyo musu tsumburewa.

Amma yawan hantara kan sa yaro ya kasa yin tsawo kamar yadda ya kamata, lamarin da kan jefa su cikin damuwa.

Saboda ko da yaro yana samun sinadaren da yake bukata na abinci da za su taimaka masa ya girma, amma kuma idan yana fama da damuwa ba za su yi wannan aikin ba.

A cewar likitoci, jikin yaro kan mayar da sinadaren zuwa ga bukatar da yaron yake da ita ta damuwa.

Haka kuma a wasu lokuta, cututtukan da suka yi kamari su ma suna taimakawa wajen tsumburewar yara.

Matsalar tana da girma a nahiyar Afrika, inda a Najeriya kuma ta fi kamari a arewacin kasar.

Hukumar lafiya ta duniya, WHO, ta yi kiyasin cewa matsalar ta shafi yara miliyan 162 'yan kasa da shekara biyar, a fadin duniya.

Inda ta yi hasashen cewa idan ba a dauki matakan da suka dace ba, kuma matsalar ta ci gaba, a shekarar 2025 za a samu yara 'yan kasa da shekara biyar miliyan 127 da za su tsumbure.