Amsoshin Takardunku - Tarihin Sarauniyar Ingila Elizabeth
An wallafa
Latsa nan domin sauraren shirin
A filin Amsoshin Takardunku na wannan makon da Buhari Muhammad Fagge ya gabatar an amsa tambayoyi biyu.
Ta farko kan Tarihin rayuwar Sarauniyar Ingila Elizabeth da ta shiga shekara ta 70 a kan karagar mulki a makon jiya ranar 5 ga watan Fabrairun.
Sai kuma tambaya ta biyu wadda aka nemi a tambayi masana shari'a ko kundin tsarin mulkin Najeriya ya yarda a bai wa wanda ya amsa laifinsa gaban kotu lauya domin ya kare shi.
Raliya Zubairu ce ta karanta tarihin yayin da Barista Zainab da ke aiki da babbar kotun Jihar Sokoto ta masa daya tambayar.