Lafiya Zinariya: Kashi 80 'na masu suna fama da kwarnafi'
Latsa hoton da ke sama domin sauraren shirin:
Kwararrun likitoci sun ce mafiya yawan mata masu juna biyu sun fi saurin samun matslar kwarnafi da kuma mutanen da kiba ta yi musu yawa.
Inda suka yi karin haske da cewa ana samun kwarnafi ne idan aka samu matsala da wani murfi wanda ke rufe tumbin a ciki.
Idan murfin bai rufu ba sai wani sinadari da ake cewa acid ya kwararo cikin bututun makoshi.
Hakan ne ke haifar da zafi da kuma radadi ko suya da mutum kan ji a kirji.
Masana sun ce kwarnafi ba shi da wata alaka da zuciyar mutum, kamar yadda wasu ke dauka cewa suna jin zafin ne a kahon zuci.
Sai dai masana a fannin kiwon lafiya sun bayyana cewa kwaranfi na iya lalata bututun makoshi kuma idan yayi tsanani ta kan kai har sai an yi wa mutum tiyata.
Hakazalika, kwarnafi na janyo cutar daji ko da yake ba kasafai ake samun hakan ba.
Hukumar lafiya ta Burtaniya ta bayar da shawara kan wasu matakai da mutum zai iya dauka a kashin kansa don samun saukin kwarnafi.
Matakan sun hada da:
- Cin abinci kadan-kadan kuma akai-kai.
- Rage kiba da samun lokacin hutawa.
- Kwanciya a kan gadon da aka dago samansa da inci takwas don kai da kirji su dago sama lokacin da mutum ke kwance, saboda kada sinadarin acid ya dawo bututun makoshi.
- Guje wa duk wani abinci da ke tayar miki da kwarnafi, kamar abinci mi yaji ko maiko ko shan taba ko kuma giya.
Sai dai hukumar ta ce idan ciwon bai tafi ba duk da daukar wadannan matakai, ya dace mutum ya je asibiti don ya ga likita.