Ra'ayi Riga: Halin da nau'in korona na Omicron ya jefa matafiya

Bayanan sautiRa'ayi Riga: Halin da nau'in korona na Omicron ya jefa matafiya
An wallafa

Latsa hoton sama ku saurari Shirin Ra'ayi Riga

Shirin Ra'ayi Riga na wannan makon ya tafka muhawara ne kan irin halin da nau'in korona na Omicron ya jefa matafiya a ƙasashen duniya, musamman Najeriya.

Ƙasashen Saudiyya da Birtaniya da Kanada sun hana matafiya daga Najeriya shiga ƙasashensu saboda Omicron, matakin da aka bayyana da cewa "na wariya" ne.