Gane Mini Hanya: Gwamna Matawalle ya gabatar da buƙatun Zamfara a taron sauyin yanayi
An wallafa
Latsa hoton sama ku saurari Shirin Gane Mini Hanya
A ranar Juma'a ne aka kawo karshen taron Majalisar Dinkin Duniya (MDD) kan sauyin yanayi a birnin Glasgow na Birtaniya.
Gwamnatoci da kwararru ne suka hadu domin samun mafita game da yadda duniya ke kara dumama da nufin samo hanyoyin warware matsalolin.
Gwamnan Jihar Zamfara a Najeriya, Bello Muhammad Matawalle, shi ma ya halarci wannan taro, inda ya gabatar da bukatun jiharsa.
A cikin wata hira da Ahmad Abba Abdullahi, ya fara ne da yi masa bayani kan abubuwan da ya gabatar a wajen taron, kafin su tattauna kan kalubalen tsaron da jiharsa ke fuskanta.