Gane Mini Hanya kan toshe layukan waya a Zamfara

Bayanan sautiGane Mini Hanya kan toshe layukan waya a Zamfara
An wallafa

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Gwamnan jihar Zamfara Bello Muhammad Matawallen Maradun ya yi kira ga takwarorinsa gwamnonin jihohin da ke makwabtaka da jiharsa da su ma su dauki matakin toshe kafofin sadarwa a jihohinsu a zaman hanyar kawo karshen bala’in ‘yan bindiga a yankin.

Gwamnan wanda ya bayyana hakan a cikin wata kebantaciyyar da sashen Hausa na BBC a gidansa da ke Gusau, ya sha alwashin tsawaita matakin toshe layukan sadarwar a jiharsa ta Zamfara daga wa’adin makonni biyu wanda ya kare da tsakar daren jiya.

A hirar wadda ya yi da Haruna Shehu Tangaza, Gwamna Matawalle ya fara ne bayanin yadda y ace toshe wayar ya taimaka wajen kubutar da daliban makarantar Kayar Maradun daga hannun ‘yan bindiga a ranar Lahadin da ta gabata: