Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Gane Mani Hanya: Jayayya tsakanin kudu da arewa kan mulkin 2023 ba ta da amfani - Bagudu
An wallafa
Latsa hoton sama ku saurari Shirin Gane Mani Hanya da Gwamnan Kebbi Atiku Bagudu
Shirin Gane Mani Hanya na wannan makon ya yi hira ta musamman da Gwamna Atiku Bagudu na Jihar Kebbi.
Cikin hirar da Haruna Ibrahim Kakangi ya yi da shi, gwamnan ya tattauna kan abubuwa da dama da suka haɗa da siyasar 2023 da kuma makomar siyasarsa.