Lafiya Zinariya: 'Sau tara ina yin ɓarin ciki'
Latsa hoton da ke sama domin sauraren shirin:
Ɓarin ciki wani abu ne da ya zama ruwan dare a tsakanin mata a Najeriya.
A wasu lokutan har wasu su kan fara camfa abin da danganta shi da abubuwa kamar shafar aljanu ko sammu.
Sannan mata musamman daga yankunan karkara ba su faye son zuwa asibiti ko cibiyoyin lafiya don gano me ke sanya su yawan ɓari ba.
Shirin na wannan makon ci gaba ne kan na makonni biyu da suka gabata, sai dai a wannnan makon an tattauna ne da wata mace da ta yi ta fama da ɓarin ciki har sau tara.
Shirin Lafiya Zinariya na wannan makon ya yi hira ne da wata mace da ta yi ta fama da ɓarin ciki har sau tara, sannan kuma ta haifi yara biyu babu rai cikin haihuwa ukun data yi.
A yanzu dai ƴa ɗaya gare ta a raye. Sai dai ta ce ba ta fitar da ran samun wasu ƴaƴan ba don kuwa tana ci gaba da neman haihuwar da son magance yawan ɓarin da atke fama da shi.

Alamomin ɓari
Likitoci sun bayyana cewa mai ciki za ta ga wasu alamomi da ke nuna mata cewa ta yi ɓari.
Wasu daga cikinsu sun hada da ciwon mara da zuban jini ko fitan gudan halittar mutum ko zuban ruwan da dan tayi ke kwanciya a ciki.
Sannan duk wasu alamu da mai ciki ke ji da suka hada da tashin zuciya da kasala duk za ta daina jinsu.
Bincike ya nuna cewa bari babbar matsala ce a Najeriya, inda kashi 30 cikin dari na masu juna biyu ke yin bari.
A likitance cikin da ya zube kasa da wasu 'yan makonni da samunsa, shi ake kira bari.
Kuma hakan ya bambanta a tsakanin mata a sassa daban-daban na duniya.
Likitoci sun bayyana cewa a kasashe masu tasowa da suka hada da wasu kasashen Afrika, macen da cikinta ya zube kafin makonni 28 shi ake kira bari.
Yayin da a nahiyar Turai kuma a kan ce mace ta samu bari ne idan cikinta da ya zube kafin mako 24 ba.
Cikin da ya zube kafin mako 22, shi ake dauka an yi barinsa a Amurka.
Masana a fannin kiyon lafiya na bayar da shawarar cewa, duk macen da ta ga wani alamu na bari ta garzaya asibiti.
Hakan a cewarsu yana da muhimmanci saboda kaucewa matsalolin kiwon lafiyar da ka iya biyo baya.
Manya daga cikin wadannan matsaloli su ne na zuban jini mai yawa, wanda hakan ka iya shafar zuciya da koda.
Haka kuma kwayoyin cuta za su iya shiga jikinta, ko mahaifarta ta fashe idan wanda ba kwararre ba ya yi mata wankin ciki.
Sannan akwai yiwuwar idan mace ta yi bari ta sake yin wani.












