Deji Adeyanju: Za mu je kotu kan dakatar da amfani da Twitter a Najeriya

Bayanan bidiyo, Deji Adeyanju: Za mu je kotu kan dakatar da amfani da Twitter a Najeriya
An wallafa

Fitaccen matashin nan da ke rajin kare hakkin dan adam a Najeriya Deji Adeyanju ya ce bai kamata gwamnatin Muhammadu Buhari ta dakatar da amfani Twitter ba.

Ya shaida wa BBC cewa da zarar kotuna sun koma yajin aikin da suke yi za su garzaya gabansu domin shigar da kara kan matakin da gwamnatin Najeriya ta dauka na dakatar da amfani da shafin.

A cewarsa, hakan ya keta hakkin adam adam "kuma yanzu ba lokacin soja ba ne."