Gane Mini Hanya 05/06/2021: Abin da ya sa ma'aikatan gwamnati ke bayyana ƙadarorinsu

Bayanan sautiGane Mini Hanya 05/06/2021: Abin da ya sa ma'aikatan gwamnati ke bayyana ƙadarorinsu
An wallafa

Ku latsa hoton da ke sama don sauraron shirin:

Bisa tsarin aikin gwamnati dai, ya kamata duk wani ma’aikaci ya bayyana kadarar tasa ta yadda da an gan shi yana kashe abin da wuce kima za a iya bincikarsa.

Farfesa Muhammad Awwal, shugaban hukumar Da’ar Ma’aikata ta Najeriya ya shaida wa Usman Minjibir cewa a yanzu haka sun mika takardun gurfanarwa na ma’aikata fiye da dari shida a gaban kotun Da’ar ta Ma’aikata bisa rashin bayyana kadara ko kuma rashin Da’a.

To sai dai farfesa Awwal ya fara bayanin ne da ayyukan hukumar tasa.