Gane Mani Hanya: Halin da makarantun tsangaya da Jonathan ya gina ke ciki a Sokoto
An wallafa
Latsa hoton sama ku saurari cikakken rahoton Haruna Kakangi
Shirin Gane Mani Hanya na wannan makon ya yi duba kan Halin da makarantun tsangaya da tsohon Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya gina suke ciki a Jihar Sokoto.
Gwamnatin Goodluck Jonathan ta yi ikirarin gina makarantu akalla 157 a fadin Najeriya a wani yunkuri na kawar da bara da kuma haɗa ilimin zamani da na addini.
Lamarin ya sa iyaye da dama murna domin kuwa suna ganin wata dama ce da ‘ya’yansu za su samu ilimin addini da na zamani a lokaci guda.
Sai dai cikin rahoto na musamman da Haruna Ibrahim Kakangi ya haɗa, za ku ji yadda almajiran da ke karatu a makarantar suke fama da bara duk da cewa an gina ta domin tsugunar da su da zummar hana su yawon barar.