Lafiya Zinariya; hira da likita kan kansar bakin mahaifa
An wallafa
Ku latsa hoton da ke sama don sauraron hirar:
Cutar daji ko kansa na iya kama ko wane sassa na jikin mutum, kuma a mata an fi ganinta a mama da mahaifa da bakin mahaifa da ciki.
Duk shekara, cutar kansa na kashe miliyoyin mata a faɗin duniya.
Wannan ya sa aka dage wajen gano riga-kafin cutar kansar bakin mahaifa wadda ita ce ta huɗu a cutukan kansa da suka fi kama mata.