Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Lafiya Zinariya, hira da likita kan yadda masu cutar gushewar hankali ke ji
An wallafa
Dakta Ɗayyiba Shaibu, ƙwararriya a ɓangaren lafiyar ƙwaƙwalwa ta asibitin The Oleaster da ke Abuja, babban birnin Najeriya ta yi bayani kan cutar gushewar hankali- alamominta da mutanen da suka fi gamuwa da wannan matsala da hanyoyin da ake bi a taimakawa masu wannan matsala a asibiti.