Gane Mani Hanya: Hanyoyin maganace rikicin Kudancin Kaduna
An wallafa
A Najeriya, a wannan makon ne aka kammala wani babban taron neman zaman lafiya a Kudancin jihar Kaduna.
A ‘yan shekarun nan dai yankin ya yi kaurin suna wajen fama da rikice-rikice da kan janyo asarar rayuka da dukiyoyi.
A cikin Shirin Gane Mani Hanya na wannan makon, Yusuf Tijjani ya shirya wata tattaunawa ta musamman da wasu wakilan al’umma da suka halarci taron kan yadda za’a kawo karshen tashe-tashen hankali a yankin.