Gane Mani Hanya: Ba zan yi takarar shugaban ƙasa ba a 2023 – El-Rufai

Bayanan sautiGane Mani Hanya: Ba zan yi takarar shugaban ƙasa ba a 2023 – El-Rufai
An wallafa

Latsa hoton da ke sama don sauraron cikakkiyar hirar

A cikin shirin Gane Mani Hanya na wannan makon, Gwamna Nasir El-Rufai na Jihar Kaduna ya ce ba zai yi takarar shugaban ƙasa ba a zaɓen 2023.

Gwamnan ya ce yana ganin ya kamata mulki ya koma kudancin Najeriya idan Shugaba Muhammadu Buhari ya kammala wa'adinsa na biyu.