Lafiya Zinariya: Matsalar Yoyon Fitsari a tsakanin mata
Latsa alamar lasifika domin sauraron shirin:
Hukumar lafiya ta Duniya, duk shekara tsakanin mace 50,000 zuwa 100,000 ne ke gamuwa da matsalar yoyon fitsari a lokacin haihuwa.
Haka kuma, hukumar ta yi kiyasin cewa mata miliyan 2 ne ke fama da ciwon a nahiyar Asiya da kasashen yankin Afrika kudu da hamadar sahara.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce, yoyon fitsari na faruwa ne idan aka samu tsagewa a hanyar da jariri ke fitowa daga jikin mahaifiyarsa saboda nakuda mai tsawo ba tare da samun kulawar malaman jinya ko likitoci ba.
Yoyon fitsari dalilin haihuwa na aukuwa ne a tsakankanin mata marasa galihu musamman wadanda ke rayuwa a yankunan da babu isassun asibitoci.
Mafi yawan matan da kan gamu da wannan matsala matasa ne kuma wadanda ba su yi karatun boko ba sannan da yawa daga cikinsu bas a neman taimako a asibiti.
Wannan ba ya rasa nasaba da tsoro ko kunya ko fargabar fuskantar tsangwama dalilin cutar a cewar Majalisar Dinkin Duniya.