Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Gane Mini Hanya 18/04/2020
An wallafa
Latsa lasifikar da ke sama don kallon bidiyon:
A yayin da kasashen duniya ke ci gaba da daukar matakan yaki da cutar corona, likitoci da sauran jami’an kiwon lafiya su ne a sahun-gaba a wannan fagen daga, kuma da dama daga cikinsu na cewa suna shiga cikin mawuyacin hali a asibitoci da kuma gidajensu bayan tashi aiki.
Dr Hadiza Sulaiman Gachi, wata likita ce ‘yar Najeriyaa da ke aiki a Asibitin George Elliot da ke Burtaniya, kuma cikin wata hira da Bara’atu Ibrahim ta bayyana mata irin kalubalen da suke fuskanta;