Gane Mini Hanya 18/04/2020

Bayanan sautiGane Mini Hanya 18/04/2020
An wallafa

Latsa lasifikar da ke sama don kallon bidiyon:

A yayin da kasashen duniya ke ci gaba da daukar matakan yaki da cutar corona, likitoci da sauran jami’an kiwon lafiya su ne a sahun-gaba  a wannan fagen daga, kuma da dama daga cikinsu na cewa suna shiga cikin mawuyacin hali a asibitoci da kuma gidajensu bayan tashi aiki.

Dr Hadiza Sulaiman Gachi, wata likita ce ‘yar Najeriyaa da ke aiki a Asibitin George Elliot da ke Burtaniya, kuma cikin wata hira da Bara’atu Ibrahim ta bayyana mata irin kalubalen da suke fuskanta;