Ku ba mu labaranku: Wace matsala ce kuka ci karo da ita kan abin da ya shafi ɓangaren lafiya?
Za mu so mu ji labarai na wasu abubuwa da suka same ku masu alaƙa da matsalar ɓangaren lafiya; alal misali samun tarnaki ta hanyar amfani da fasaha a harkokin lafiya ko ƙarancin albashi ga ma’aikata ko rashin fasahar sadarwa da ingantattun ayyukan lafiya ko ƙaruwar tsadar kuɗin asibiti ko ƙarancin ma’aikatan lafiya.
Ku cike fom din da ke ƙasa idan kuna son ku ba mu wani labari na halin da kuka shiga dangane da matsalar ɓangaren lafiya. Za mu ɓoye sunanku idan har ba kwa so mu wallafa. Ku saka lambar waya da adireshin imel ɗinku ta yadda za mu tuntuɓe ku don samun ƙarin bayani. Idan har labarinku ya cancanci a wallafa shi, to ɗaya daga cikin ma’aikatanmu za su tuntuɓe ku.