Ku ba mu labaranku: Wace matsala ce kuka ci karo da ita kan abin da ya shafi ɓangaren ilimi?
Za mu so mu ji labarai na wasu abubuwa da suka same ku masu alaƙa da matsalar ɓangaren ilimi; alal misali tarnaƙi ta ɓangaren ƙarancin kuɗaɗe ko yajin aiki ko matsalar tsaro ko cin hanci ko rashin shugabanci nagari ko ƙarancin kayan more rayuwa ko tsadar kuɗin karatu ko ƙarancin kayan koyarwa ko kuma siyasantar da harkokin Ilimi.
Ku cike fom din da ke ƙasa idan kuna son ku ba mu wani labari na halin da kuka shiga dangane da matsalar ɓangaren ilimi. Za mu ɓoye sunanku idan har ba kwa so mu wallafa. Ku saka lambar waya da adireshin imel ɗinku ta yadda za mu tuntuɓe ku don samun ƙarin bayani. Idan har labarinku ya cancanci a wallafa shi, to ɗaya daga cikin ma’aikatanmu za su tuntuɓe ku.