Ku ba mu labaranku: Ta yaya matsalar tsaro da rikice-rikice ke shafarku?
Wace matsalar rashin tsaro kuka samu kanku a ciki, kama daga tashe-tashen hankula a birane da karkara da satar Mutane don kudin fansa da cin zarafi da fashi da makami da rikicin ƙabilanci da faɗan daba? Ku cike fom din da ke ƙasa idan kuna son ku ba mu wani labari na halin da kuka shiga dangane da matsalar rashin tsaro. Za mu ɓoye sunanku idan har ba kwa so mu wallafa. Ku saka lambar waya da adireshin imel ɗinku ta yadda za mu tuntuɓe ku don samun ƙarin bayani.
Idan har labarinku ya cancanci a wallafa shi, to ɗaya daga cikin ma’aikatanmu za su tuntuɓe ku.