Za a yi adalci wajen fitar da ɗan takara a NNPP- Kwankwaso
An wallafa
Latsa hoton da ke sama domin kallon wannan bidiyon
Mai neman jam'iyyar NNPP ta tsayar da shi takarar shugaban kasa, kuma jagoran jam'iyyar a Najeriya Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya ce rububin da 'yan siyasa suke yi wajen shiga jam'iyyar ba zai zame musu matsala ba, idan an zo tsayar da 'yan takara.
A tattaunawarsa da abokin aikinmu Yusuf Ibrahim Yakasai, Sanata Kwankwaso ya ce jam'iyyar ta su tana da kyawawan tsare-tsare wajen fitar da yan takara, da ya ce ya bambanta da na sauran jam'iyyu.