Bidiyon Ku san malamanku tare da Sheikh Khuzaima Isma'ila Idris

An wallafa

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Iyayen Malam Khuzaima Isma'ila Idris bin Sulaiman, Ardo Abdullahi asali mutanen Jahun ne, daga bisani suka koma Jihar Bauchin Najeriya.

Amma shi Malam Khuzaima an haife shi ne a garin Jos a unguwar Dodo. Ya fara neman ilimi daga wurin mahaifinsa na addini da boko.

Ya yi karatun addini a wajen yayarsa mai suna Basma, saboda girma da rashin lafiya da ta samu mahaifinsu, wanda ya sanya ba zai iya ci gaba da koyar da su ba.