Bidiyon Ku san malamanku tare da Sheikh Khuzaima Isma'ila Idris

Bayanan bidiyo, Ku san malamanku tare da Sheikh Khuzaima Isma'ila Idris
An wallafa

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Iyayen Malam Khuzaima Isma'ila Idris bin Sulaiman, Ardo Abdullahi asali mutanen Jahun ne, daga bisani suka koma Jihar Bauchin Najeriya.

Amma shi Malam Khuzaima an haife shi ne a garin Jos a unguwar Dodo. Ya fara neman ilimi daga wurin mahaifinsa na addini da boko.

Ya yi karatun addini a wajen yayarsa mai suna Basma, saboda girma da rashin lafiya da ta samu mahaifinsu, wanda ya sanya ba zai iya ci gaba da koyar da su ba.