Yakin Ukraine: Kamfanonin kasashen Yamma da suka fice da wadanda ke Rasha har yanzu

TotalEnergies company logo is seen on its head office building on February 10, 2022 in La Defense business district near Paris, France.

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

Tun bayan mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine, kamfanonin kasashen yamma da dama kamar Apple da Disney da kuma Netflix sun daina kasuwanci a Rasha.

Wasu kamar babban kamfanin man fetur na Shell sun sanar da za su fice da ga kasar a hankali a hankali, yana ba da misali da ƙalubalen da ayyukansa ke fuskanta a Rasha ta fuskar tattalin arziki.

Kuma waɗanda suka iirn su McDonald's da Coca-Cola suna fuskantar kiraye-kirayen ficewa daga Rashar a matsayin martani ga mamayar da Shugaba Putin ya yi wa makwabciyarsa Ukraine.

To su waye suka tafi kuma su waye suka tsaya?

'Abin buƙatar rayuwa'

Kamfanin makamashi na Faransa Total Energies ya ƙi ya janye hannun jarinsa daga Rasha kamar yadda takwarorinsa BP da Shell suka yi.

A halin yanzu, mamallakin kamfanin kayan sawa na Japan mai suna Uniqlo ya kare matakinsa na barin shagunansu na Rasha a bude, inda ya ce tufafi ''abin buƙatar rayuwa ne''.

Shoppers are seen at the Japanese clothing brand Uniqlo store in Hong Kong. (Photo by Budrul Chukrut/SOPA Images/LightRocket via Getty Images)

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mamallakin kamfanin Uniqlo ya ce ''Rashawa na da hakkin rayuwa kamar yadda muke da''

Tadashi Yanai, mamallakin kamafanin Uniqlo, ya fada wa jaridar Nikkei cewa ''Rashawa na da hakkin rayuwa kamar yadda muke da shi''.

''Bai kamata a ce ana yaƙi ba, ya kamata kowace ƙasa ta yi adawa da hakan."

Amma ya kara da cewa "tufafi wajibcin rayuwa ne, kuma Rashawa na da hakkin rayuwa kamar yadda muke da shi."

Amma kamfani kamar Uniqlo na ci gaba da shan matsin lamba a gida da ya ƙaurace wa Rasha bisa mamayar da ta ke yi wa Ukraine.

Fuskantar kauracewa

Maudu'an neman ƙauracewa kamfanonin #BoycottMcDonalds da #BoycottCocaCola sun yi ta tashe a Twitter ranar Litinin da kuma a ƙarshen mako.

Deborah Meaden, wata mai hannun jari a shirin BBC mai suna Dragon's Den ta nemi mutane a shafukan sada zumunta da su daina shan Coca-Cola.

Meaden ta ce "mu nuna musu karfin ikon mutane."

McDonald's da Coca-Cola da KFC da Pepsi da Starbucks da kuma Burger King duk sun ƙi yin magana da BBC.

Mafi yawan kamfanonin da BBC ta tuntuɓa suna da manyan kantuna a ƙasar.

Kantin abinci na KFC yana da rassa 1,000 a fadin Rasha a ƙiyasin da aka yi bara.

A wani bayani da ya wallafa a shafinsa na intanet kwanan nan, kamfanin McDonald ya ce yana da kantuna 847 a Rasha.

Kauce wa X
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X

'Kasuwanci mai sarƙaƙiya'

Kathleen Brooks, Darakta a cibiyar bincike ta Minerva ta ce, kasacewar kasuwancin McDonals's da Coca-Cola na da sarƙaƙiya ya sa barin Rasha cikin gaggawa ya zama musu abu mai wahala.

Ta shaida wa BBC cewa Coca-Cola na da tsari mai ban mamaki a Rasha inda yake da wuraren sarrafawa da dama.

Amma a ranar Talata ta ce kamfanin zai dakatar da aiki a kasar, wanda yake kusan kashi 2 cikin 100 na kudin shigar da kafanin ke samu. Kuma yana da kusan kashi 20 cikin 100 na samar da robobi a kasar.

Food courier outside the first McDonald's that opened in Russia

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Reshen McDonald's mafi tsufa da ke kusa da Pushkin Square a Moscow, tun 1990

Duk da cewa ba wai gwamnatin Faransa na tursasa wa kamfanonin barin Rasha ba ne, Shugaba Macron ya sha bayyana wa shugabannin kamfanoni cewa zama a kasar zai ƙara tsanani in aka ci gaba da yaƙin, a cewar jaridar Birtaniya 'Financial Times'.

Shugaban Faransa ya gana da shugaban bankin Societe General Danone da kuma kungiyoyin 'yan kasuwa a kan batun.

'Kima sama da Riba'

Sannan a ranar Talata kamfanin Shell ya ce zai gaggauta daina sayen mai daga Rasha kuma zai janye ayyukansa daga kasar.

A wata sanarwa, kamfanin ya kuma ce zai rufe wuraren ayyukansa da wurin ba da man jirgi da kuma wurin kula da injinan ababen hawa.

Kamfanin ya ba da hakuri bisa sayen jirgin dakon mai daga Rasha a satin da ya gabata.

Shell ya riga ya bayyana shirinsa na yanke huldar hadakarsa da kamfanin makamashi na Rasha biyo bayan mamayar.

Worker at Shell petrol station in Russia

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Shell ya ce zai rufe gidajen man sa dama sauran ayyukan sa a Rasha

Susannah Streeter, babbar mai hasashe kan zuba jari da kasuwanci a Hargreaves Lansdown ta ce kamfanin ya zabi ya kare ƙimarsa fiye da neman ya samu riba.

Amma ta bayyana wahalar da ke tattare da kawar da ayyukansu daga kasuwar Rashar.

Ficewar ɗumbin jama'a

Kamfanonin kasashen yamma da yawa sun sanar da za su daina aiki a Rasha.

Babban kamfanin zuba jari a Rasha BP ya sanar cewa zai sayar da kashi 20% na iskar gas da ya mallaka karkashin kamfanin albarkatun iskar gas na Rasha.

Wannan matakin zai kawo karshen huldar kasuwanci na tsawon shekara 30.

Kamfanin ExxonMobil ya bi sawu wajen dakatar da ayyukansa na mai da iskar gas.

Amma ficewar kamfanonin ya shafi sauran sassa.

A re:Store shop at the Metropolis shopping mall. re:Store is the largest retail chain of Apple branded stores in Europe with Apple Premium Reseller (APR) sta

Asalin hoton, Getty Images

A farkon wannan watan ne, kamfanin Apple ya dakatar da sayar da dukkan kayansa a Rasha, tare da fadin yana goyon bayan mutanen da ke shan wahala a dalilin yaki.

Kamfanin Microsoft ma ya dakatar da sayar da kayansa kuma kamfanin Google ya cire wadanda suke daukar nauyin wallafe-wallafe na Rasha.

Kamfanonin samar da kayan wasanni kamar Nike da Puma da Chanel sun dakatar da saye da sayarwarsu tare da rufe kantunansu.

Wasu kamfanonin kamar na kayan ƙawa ma irin su Burberry da Chanel da H&M da kuma Zara.sun dakatar da saye da sayarwa

Burberry in Red Square

Asalin hoton, Getty Images

Kamfanonin shirya fina-finai irin su Warner Bros da Disney da Sony sun dakatar da sakin fina-finansu a sinimomin Rasha.

Manyan kamfanonin dakon kaya na duniya kamar Danish Maersk da Geneva-based MSC sun dakatar da fitar da shigar da kwantenonin kaya Rashan.

Su ma kamfanoni irin su Visa da Mastercard da kuma Volkswagen sun daina hada-hadar kasuwanci da Rasha.