David Fuller: 'Yan matan da suka mutu a hadarin mota aka kuma yi lalata da gawarsu

Asalin hoton, Family handout
- Marubuci, Dag Catherine Burns
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
- An wallafa
Nike Akande na ci gaba da jin radadi a zuciyarta. Shekaru shida da suka gabata, mijinta ya rasu, da 'ya'yanta mata biyu a mummunan hatsarin mota.
A yanzu tana cikin bakin ciki, da kokarin farfadowa daga tashin hankalin da ta samu kanta a ciki bayan samun labarin David Fuller ya ci razafin gawar 'ya'yanta ta hanyar lalata.
Shekarar Mary 16. 'Yar uwarta Helen kuma shekararta 22.
A birnin Paris na Faransa suke da zama, amma a shekarar 2014 suka tafi Birtaniya tare da iyayensu jim kadan bayan kammala hutun Ista.
Suna cike da zakwadin yawo a birnin Landan da sayayya a shaguna daban-daban, sun ma shirya zuwa fitaccen kantin Primark.
Amma jim kadan bayan sun sauka daga jirgin ruwan da ya kawo su, sai wata a kori-kura ta daki motarsu a kan titin Kent.
Nan take suka mutu. Mahaifinsu da ke cikin motar ya rasu bayan makwanni biyu da hadarin. Ni ce kadai ta kubuta.
'Ina kaunarki Mama'

Lokacin da Nike ke bayanin yadda hatsarin ya faru, alamu sun nuna ta sha ba da labarin bila adadin.
Muryarta cike da damuwa, ta bayyana lokacin da ta bai wa 'ya'yan nata alawa a lokacin da suke cikin motar.
Mary ta yi mata godiyata tare da cewa "Maman, je t'aime", da harshen Faransanci wato ''Mama. Ina kaunarki.''
Amma da hirar ta koma kan batun David Fuller, sai Nike ta yi sharaf kan kujera, tare da rufe idanunta, kamar tana kokarin daina jin abin da aka yi magana.
Bacin ran da ya bayyana a fuskarta ba zai misaltu ba. Sai ta kada baki ta ce: "Ba wanda ya cancanci haka. Wannan bai dace."
Mai gyaran wutar lantarki a asibiti, Fuller ya kashe mata biyu a Tunbridge Wells a shekarar 1987.
Sannan ya ci zarafin gawar mata sama da 100 ta hanyar lalata da su, ciki har da yara a dakin ajiyar gawawwaki biyu da ke kent cikin shekara 12. Ciki har da Mary da Helen.
Iyalan sun niƙi gari tun daga Faransa a lokacin annobar korona domin sauraren ƙarar da hukuncin da za a yanke masa. Ba zai taba fitowa daga gidan kaso ba.
A cikin kotun, iyalan matan sun bayyana abin da Fuller ya yi da ''aikin dabbanci,'' sannan sun ce shaidani ne, kuma maketaci.
Wannan shi ne karo na biyu da iyalan Akande suka halarci zaman kotun ta Crown Court da ke Maidston, domin ganin irin hukuncin da za a yanke wa mutumin kan abin da ya faru da Mary da Helen.
A shekarar 2015 aka yanke wa direban a kori-kurar da ya daki motarsu Mary hukunci.

Asalin hoton, Family handout
'Yar Nike mai suna Audrey ce ke taimakon ta. Ta ce ta na jin kamar sau biyu aka kashe mata 'yan uwa, a lokacin da aka fada mata abin da Fuller ya aikata na cin zarafin gawar 'yan uwanta ta hanyar lalata da su.
Ta tuna abin da ta fada a lokacin "Kai wannan wasa ne, sai ka ce a shirin fim?"
Da ƙyar ta iya karasa maganar: "Saboda - gawa ce fa? Wai me ke faruwa ne?"
"Wannan mummunan mafarki nake yi, ƙarya ne. wannan ba abin da zai yiwu ba ne."
'Aikin shaidan'
Audrey na da juna biyu, amma ta kafe kan lallai "tana son ganin mutumin" ido da ido.
Iyalan mabiya addinin Kirista ne, kuma Nike ta ce idan har za ta iya magana da Fuller, abin da za ta fada masa shi ne, "yana bukatar Allah, yana bukatar Yesu Almasihu.''
Ta bayyana abin da ya aikata da aikin shaidanu, amma duk da hakan za ta yafe masa.
Amma ga Audrey babu wani batun yafiya. Tana son sanin me ya sa Fuller ya yi musu haka da sauran iyalai.
Ta ce tana son yin magana da BBC, saboda tana ganin 'yan uwanta sun cancanci a yi wani abu na jinjina musu.

Asalin hoton, Family handout
Abu ne mai matukar wuya a gare ta. Ta yi ta faduwa tare da ɓarkewa da kuka. Akwai lokacin da ko magana ta gagara yi.
Amma ta bayyana ƙannenta da 'yan mata kyawawa abin sha'awa".
Sai ta yi dariya yayin da hawaye ke zuba a kuncinta, tana kallon hotunan Helen, tana tuno yadda take jiƙa banɗaki da ruwa idan ta shiga wanka.
Ta bayyana Mary da furen gidansu, abar so ga kuwa. Tana shan yabo ga duk wadanda suka hadu da ita.
Ta kuma bayyana yadda Helen da Mary ke faranta wa ƴan gidansu.
Ta kara da cewa: "Duk da cewa muna raye. Amma rayuwarmu ta taƙaita, ba ma farin ciki, babu wata walwala ko annashuwa a tare da mu."










