Mutumin da ya bayar da sadakar kashi 15 cikin 100 na albashinsa

John Yan

Asalin hoton, John Yan

Bayanan hoto, John Yan y ce ya na son taimakawa masu karamin karfi da ba su da abin da ya mallaka
    • Marubuci, Daga Suzanne Bearne
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Business reporter
  • An wallafa

John Yan ya yanke shawarar ya fara ba da sadakar kashi 15 cikin 100 na albashin da yake dauka a duk shekara, duk da cewa idan ya kai shekarun tsufa zai yi aiki tukuru.

Matashin mai shekara 27, injiniyan manhajar na'ura mai kwakwalwa, wanda ya fara da kashi 1 cikin 100, daga bisani a shekarar 2020 ya kar zuwa kashi 3, kafin a cikin shekarar nan ya karu zuwa kashi 15.

"A takaice wannan matakin da na dauka na nufin ba zan yi ritaya da wuri ba," in ji Mista Yan, mazaunin birnin New York, da kuma ya ke aiki nan.

"Watakil ma nan gaba ba zan iya kai 'ya'yana makarantar kudi ba, si dai ta gwamnati."

Yana sanya kudin sadakar ne ga wani asusun tallafi mai suna Giving What We Can (GWWC). Asususn na bai wa mutane kwarin gwiwar yin sadaka da kashi 10 cikin 100 na albashinsu.

Mambobin za su iya bada sadakar kai tsaye ga asusun da suka aminta da shi, amma wanda GWWC ya ba su zabi.

Ciki har d wasu asusun tallafawa iyaye mai suna Centre For Effective Altruism - wanda aka yi wa rijista a kasashen Amirka da Birtaniya.

Tun Mista Yan ya na yaro iyayensa suka koma Amirka a matsayin 'yan ci ranin, ya ce ya san ya na samun abin da yawancin mutane ba sa samu duniya, don haka yake son ba su wani kaso daga guminsu domin ya taimaka musu.

"Na lura cewa dan abin da zan ba da, zai sanya wasu farin ciki, shi ya sa na dauki wannna matakin nan."

Kudaden kasashe daban-daban

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Za ka iya sadakar kashi 10 cikin albashin ka?

A shekarar 2009 aka samar da asusun GWWC, wand wasu daliban jami'ar Oxford Will MacAskill da Toby Ord suka samar.

Duka mutanen biyu sun zage damtse domin kirkiro hanyar da za a taimakawa mabukata.

GWWC ya yi ikirarin sama da mutum 6,000 ne suka shiga shirin, ya yin da kawo yanzu an tara sama da dala miliyan 244 na sadaka. Mambobin asusun na amfani da intanet wajen sanya kudin.

Duk da cewa annobar korona ta janyo sauyawar lamura, amma GWWC ya ce an samu karin mutanen da suka shiga asusun a shekarar da ta gabata duk da annobar da ake fama da ita.

Haka kuma mambobi sabbi 1,000 ne suka shiga duk da cewa ana korona, da dokar kulle, hakan ya nuna ana bukatar taimako a wannan tsakanin.

Sannan wasu 1,000 sun yi alkawarin sanya kashi 10 na albashinsu a asusun GWWC a shekarar 2020, d wadanda za su bada kasa da hakan.

Me ya sa za a bai wa mutane kwarin gwiwar bada sadakar kashi 10 ko kasa da hakan?

"Wannan adadin shi ne wanda ba zai takura kowa ba, da kuma mu na bukatar abin da zai dore ba na wucin gadi ba," in ji daraktan GWWC Luke Freeman.

"Dan wani bangare ne na abin da mutane ke samu na kudaden shiga, kuma mutanen da ke kasashe masu arziki za su iya tallafawa."

Ya yi kwatance da tsohuwar al'dar nan ta tarihin Yahudawa da Kiristoci na bada sadakar kashi 10 na albashinsu ga majami'u ko asusun tallafi.

Will MacAskill ya na jawabi a shirin TED a shekarr 2018

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Will MacAskill

Pippa Gilbert ya fara sanda sadakar kashi 10 na albashinsa ga asusun GWWC shekarun da suka gabata.

"Ina da abin da na ke bukata na yau da kullum, a gare ni dan abin da na ke ba dawa sadakar bai taka kara ya karya ba, ," in ji matar da ke zaune Hague, a Netherlands.

A wannan shekarar ne Mis Gilbert ta yi ritaya daga aikin da ta ke yi a matsayin mai sharhi da wata kungiya mai zaman kan ta, hkan na nufin kudin shigarta ya ragu.

"Amma duk da hakan kudin da na ke samu sun min yawa," in ji ta.

Yayin da cikin masu shiga asusun akwai dalibai, da 'yan fansho, da ma'aikatan banki, da masu zuba jari, da 'yan kasuwa, Mista Freeman ya ce mafi kankanta cikin su su ne 'yan shekara 30.

"Yayin da masu karamin karfi ke ganin muhimmancin ba da abin da ya sawwaka, mu na bai wa masu hannu da shuni karfin gwiwar su bayar," in ji Freeman.

Pippa Gilbert

Asalin hoton, Pippa Gilbert

Bayanan hoto, Pippa Gilbert, wadda ta yi ritaya a kwanan nan, ta ce ta na da abin da za ta iya ci gaba da bada kashi 10 a matsayin sadaka

Ma'aurata mazuna Boston, Julia da Jeff Wise ma'aikata ne da ke samun albashi mai tsoka, sun ba da sadakar kashi 50 ga kungiyoyin agaji, musamman wadda ke yaki da cutar Malaria.

Suna bada tallafin ne a wata gidauniya mai suna Givewell, wadda ke bincikar masu tsananin bukatar taimako domin tallafa musu.

"Ina ganin tun da kuruciya ya kamata mu dinga haka, domin taimakon masu karamin karfi," in ji Mis Wise, mai shekara 36.

Presentational grey line

Sai dai duk da haka kungiyoyi da asusu irinsu GWWC, ba sa rabo da masu sukar ayyukansu, wanda ake musu kallon masu kaucewa biyan haraji da sauransu.

Julia da Jeff Wise

Asalin hoton, Julia Wise

Bayanan hoto, Julia da Jeff Wise suna ba da kashi 50 na abinda suke samu

"Abu ne mai kyau ganin mutane na bai wa kungiyoyin agaji wasu kudade, amma wannanba dalili ne na tara kudade ba tare da biyan haraji ba," in ji Jeevun Sandher mai sharhi kan sha'anin tattalin arziki daga King's College da ke birnin Landan.

"Amurkawa sun fi sadakar wani kaso na abin da suke samu fiye da kowacce kasa (a shekarar da ta gabata sun bada sadakar dala biliyan 47) amma duk da haka, Amirkawa na fama da talauci.

"Dalilai uku na ke ganin bai dace da tsarin ba. Nafarko dan abin da ake bayarwa ba ya isar wadanda ake bayrwa dominsu.

"Na biyu, bai wa masu karamin karfi tsabar kudi ita ce kadi dorarriyar hanya ta kauda talauci.

Kungiyoyin agajin da ke bai wa mbukata abinci a makarantu da matattatarar matasa, a yankunan matalauta domin ingnra rayuwarsu.

An yi ba a yi ba domin ba za su iya musanyawa da kudin da suke bukata ba.

Sai na karshe, kudin sadkar da mutanen ke karba, ba sahihiyar hanya ce mo dorewa ba idan ana batun kudin shiga, ba abu ne da zai wadaci kowa ba."

Yara a Burkina Faso na cin moriyar irin wadannan asusu

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, GWWC na bada shawarar yin sadaka, sannan wadanda su ke asusun za su iya bai wa wanda suka ga dama

Mista Freeman ya ce har yanzu kungiyoyin agaji na taka rawa wajen sauya rayuwar masu fama da matsanancin talauci a duniya.

"Yawanci muna da arziki fiye da tunain mu, ywancinmu mu na da abin yi a ko da yaushe," in ji shi .

"Matsakaicin kudin shiga a kasashe kamar Birtaniya, na ba ka kwanciyar hankali da saukin rayuwa cikin kashi 5 na masu arzikin duniya.

Wannan kudi ka iya sauya rayuwar mutumin da ke fama da matsanncin talauci, da kusn kashi 100, fiye da inganta ta ka rayuwar."